Saura kiris a nakasa ni - Neymar

Neymar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Raunin ne ya kawo karshen rawar Neymar a gasar

Dan wasan Brazil Neymar ya fashe da kuka lokacin da yake bayyana cewa raunin da aka jima ya kusa nakasa shi.

Dan kwallon na Barcelona, mai shekaru 22, ya ji rauni a bayansa lokacin da dan Colombia Juan Zuniga ya hau bayansa a wasan da Brazil ta yi nasara da 2-1 a quarter-final.

"Na godewa Allah da ya taimake ni, saboda saura kiris ya jikkata ni," a cewar Neymar.

Brazil sun sha kayi da ci 7-1 a hannun Jamus a wasan kusa da na karshe.

Raunin na Neymar ya girgiza al'ummar Brazil baki dayansu inda aka rinka jimami da nuna damuwa kan abinda ya faru da shi.

Karin bayani