Sanchez ya koma Arsenal daga Barca

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alexis Sanchez na murnar zura kwallo a Brazil

Dan kwallon Chile, Alexis Sanchez ya sanya hannu a yarjejeniyar koma wa Arsenal daga Barcelona a kan kudi kusan fan miliyan 35.

Dan shekaru 25, ya zura kwallaye 47 cikin wasanni 141 a Barcelona kuma ya zura kwallaye biyu a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Ya ce "Ina murnar hade wa da kungiyar wacce ke da babban manaja, da zaratan 'yan wasa da kuma goyon baya a fadin duniya."

Ya kara da cewar "Na zaku ina soma buga gasar Premier da ta zakarun Turai."

Arsenal din kuma na kan hanyar sayen dan wasan Faransa Mathieu Debuchy daga Newcastle United.