Liverpool ta amince ta sayar da Suarez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suarez ya taka leda sosai a Liverpool

Luis Suarez na gab da komawa Spain bayan da Liverpool suka sanar da cewa sun amince su sayar da shi ga Barcelona akan kudi fam miliyan 75.

"A yanzu dan wasan na da damar tattaunawa da Barcelona domin kammala sauran abubuwan da suka rage," a cewar sanarwar da kulob din ya fitar.

Muna godewa Luis saboda rawar da ya taka da gudummawar da ya baiwa kulob din na kaiwa gasar zakarun Turai.

Baki dayan al'ummar Liverpool na yi wa Luis da iyalansa fatan alheri kan rayuwarsa ta gaba.

A sanarwar da ya fitar, Suarez ya ce " ina yiwa Brenden Rodgers da Liverpool fatan alheri. Kulob din na hannun kwararrun mutane kuma ina da tabbacin za su yi nasara a kakar wasanni mai zuwa".

Ana ganin batun cizon da dan wasan yayi da kuma dakatarwar da aka yi masa na daga cikin dalilan da suka sa shi barin LIverpool.

Karin bayani