Suarez: Barcelona ta amince kan fam 75m

Hakkin mallakar hoto FC Barcelona
Image caption Ya ce, ''ni da iyalaina za mu kasance magoya bayan Liverpool a ko da yaushe''

Liverpool ta amince ta sayar wa Barcelona Luis Suarez a kan kudin da ya kai fam miliyan 75, na tsawon shekaru biyar.

Dan wasan na Uruguay, mai shekaru 27 an dakatar shi daga duk wata harka ta kwallon kafa tsawon wata hudu saboda cizon Giorgio Chiellini na Italia.

A mako mai zuwa ne, Suarez wanda ya ci kwallaye 31 a Premier a kakar da ta kare, zai je Spain a gwada lafiyarsa.

A shekara ta 2011 Suarez ya koma Liverpool daga Ajax a kan fam miliyan 22.7, kuma akwai sauran shekaru hudu a kwantaraginsa.

Komawarsa Barcelona ta sa zai kasance kusa da iyalan matarsa Sofia.

''Baki dayan al'ummar Liverpool na yi wa Luis da iyalansa fatan alheri kan rayuwarsa ta gaba.'' Inji kocin kungiyar Brendan Rodgers

Karin bayani