Ingila za ta yi wasan zumunta da Sweden

Image caption Tawagar Ingila ta mata za ta gwabza ta Sweden

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta zabi 'yan wasan da za su buga mata wasan sada zumunta da Sweden.

Wasan zai bawa Kungiyar ta Ingila damar shiryawa tunkarar wasan fitowa gasar cin kofin duniya wanda za ta kara da Wales.

Kungiyar Kociya Mark Sampson za ta kara kuma da Swedes a Hartlepool a ranar 3 ga watan Agusta.

Nasarar da Ingilar ta samu da ci 2-1 a Ukraine a watan Yuni hakan na nufin Ingilar na bukatar yin wasa babu ci ne daga wasanninta biyu na rukuni.

Karin bayani