Gotze 'dan baiwa' ne - Low

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mario Gotze na murna tare da kananan yara

Kocin Jamus, Joachim Low ya jinjinawa Mario Gotze, inda ya bayyana shi a matsayin 'dan baiwa' bayan da ya zura kwallo a wasan da kasar sa ta lashe gasar cin kofin duniya.

Low ya bayyana cewar ya gayawa Gotze cewar ya nuna wa duniya ya fi Lionel Messi iya zura kwallo bayan da aka shigo da shi cikin wasa.

Jamus ta lashe kofin sau hudu kenan kuma a karon farko cikin shekaru 24.

Gotze mai shekaru 22 ya ce "Abun nada dadi, mutum ya zura kwallo a wasan karshe na cin kofin duniya."

Gotze ya koma Bayern Munich ne daga Borussia Dortmund a kan fan miliyan 31.5.