Scolari ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Scolari ya yi abun kunya a idon 'yan kasar Brazil

Mai horar da yan wasan Brazil Luiz Felipe Scolari ya yi murabus sakamakon gazawar kasarsa ta samun nasara a gasar cin kofin duniya na shekarar 2014.

Scolari mai shekaru 65 a duniya ya sami daukar kofin a shekarar 2002 sai dai kuma kasar ta Brazil wadda ta karbi bakuncin gasar ta kare ne a matsayi na hudu a takarar.

Brazil ta sha kashi da ci 7-1 a hannun Jamus a gasar kusa da na karshe.

Wannan dai shine ci mafi muni da suka taba fuskanta kuma karo na farko da aka lallasa su a cikin gida a tsawon shekaru 39 da suka wuce.

Bugu da kari sun kuma sha kashi da ci 3-0 a hannun Netherlands a takarar neman matsayi na ukku.

Da ma dai kwantaragin Scolari za ta kare ne a karshen gasar sai dai tashar talabijin ta Globo ta ruwaito cewa a yau Litinin ne hukumar kwallon kafa ta Brazil watau CBF za ta tabbatar da murabus din mai horar da 'yan wasan.

Scolari ya baiyana ranar da aka doke yan wasansa da cewa ita ce rana mafi muni a rayuwarsa.

Ya kuma nemi gafara daga jama'ar Brazil.