Gotze "dan baiwa" ne

Kociyan Jamus Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kociyan Jamus

Kociyan Jamus Joachim Low ya jinjina wa Mario Gotze a matsayin "dan baiwa" bayan kwallo 1 da ya saka a ragar Argentina cikin karin lokacin da aka yi a wasan karshe na gasar cin Kofin duniya wanda ya baiwa Jamus din nasara a kan Argentina.

Har ila yau kuma, Low ya bayyana cewa ya gaya ma Gotze cewa ya nuna ma duniya cewar ya zarce Lionel Messi 'yan mintoci kafin a yi canjin dan wasan.

Jamus dai ta samu nasarar cin kofin karo na hudua tarihi, amma kuma karon farko cikin shekaru 24.

Gotze dan shekaru 22 da haihuwa ya ce "abin ya ba ni mamaki. Ka ci kwallo ma kuma ma ba ka fahimci abinda ke faruwa ba".

Yayinda ya rage saura minti 7 karin lokaci da aka yi a wasan ya kare, dan wasan tsakiyar na Bayern Munich ya yi amfani da kafar sa ta hagu bayan ya yanke Andre Schurrles, ya zura kwallon.

"dan baiwa ne wanda ke wasa a wurare dabam-dabam, shine mai yanke hukunci, wanda zai shigo ya kawo bambanci" a cewar Low. "abinda ya yi kenan".

Gotze, wanda ya koma Bayern Munich a wata yarjejeniya da aka kulla da Borussia Dortmund a kakar wasa ta bara ya bayyana cewa "ba a ma san yadda za a bayyana shi ba." Mafarkin ya zama gaskiya.

To, sai dai duk da yake ba su samu nasara a wasan ba, Messi ne aka ce, ya zamo dan wasan da ya fi kowa haskakawa. Kociya Alejandro Sabella ya ce "lallai ya cancanta" ya kara da cewa "ya yi wasan a zo a gani a gasar cin kofin duniyar, abinda ya kai mu matsayin da ya kai mu."

Karin bayani