Chelsea ta kammala cinikin Costa

Diago Costa Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Dan kwallo na 3 da Chelsea ta dauko a bana kenan

Kulob din Chelsea ya kammala cinikin dan kwallon Atletico Madrid Diego Costa kan kudi fan miliyon 32 a yarjejeniyar shekaru biyar.

Costa mai shekaru 25 dan kwallon Spaniya shi ne dan wasa na uku da Chelsea ta dauko a bana, bayan Cesc Fabregas da Mario Pasalic.

Dan wasan ya zura kwallaye 36 a wasanni 52 da ya bugawa Atletico, a inda suka lashe kofin La Liga wanda rabon kulob din da kofin tun 1996.

Chelsea ta kare a matsayi na 3 a teburin gasar cin kofin Premier bara da maki 82.