"Man United za ta yunkuro karkashin Van Gaal"

louis van gaal
Image caption United na fatan kocin zai dawo da tagomashin kulob din

Tsohon dan kwallon Man United Bryan Robson ya ce kulob din zai dawo da tagomashinsa a karkashin sabon koci Louis van Gaal.

Van Gaal zai karbi ragamar horas da United a Old Trafford, bayan da ya jagoranci tawagar Holland kaiwa matsayi na 3 a gasar cin kofin duniya da Brazil ta dauki bakunci.

Manchester United na ziyara a Amurka domin wasannin atisaye da LA Galaxy da Roma da Real Madrid da Inter Milan kafin fara gasar cin kofin Premier.

Van Gaal ya karbi aiki a hannun David Moyes, bayan da kulob din ya sallame shi watanni 10 da fara aiki.