Chelsea na daf da daukar Felipe

Felipe Luis Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan kwallo na hudu da Chelsea ke shirin dauko a bana

Chelsea na daf da daukar Felipe

Kulob din Chelsea ya cimma yarjejeniyar sayen dan kwallon Athletico Madrid Felipe Luis.

Luis, mai shekaru 28 zai tattauna da kungiyar kafin a duba lafiyarsa domin cancantar buga kwallo a kulob din.

Dan kwallon ya buga wasanni 44 a Atletico abin da ya basu damar lashe kofin La Liga wanda rabon kungiyar da kofin tun 1996.

Chelsea na shirin dauko dan wasan ne da nufin maye gurbin Ashley Cole, wanda ya koma kulob din Roma ta kasar Italiya.