Juventus ta dauko sabon koci Allegri

Massimiliano Allegri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya taba lashe kofin Seria A a shekarar 2010/11

Kulob din Juventus ya dauko tsohon kocin AC Milan Massimiliano Allegri, domin ya horas da kungiyar.

Allegri, mai shekaru 46 wanda Milan ta sallama a watan Janairu, ya maye gurbin Antonio Conte ne wanda ya ajiye aiki ranar Talata.

Daractan Juventus Giuseppe Marotta, ya ce kulob din na hankoron ci gaba da samun nasarori domin kara yin fice a duniya.

Alegri ya lashe kofin Serie A da Milan a kakar farko da ya horas da kulob din a shekarar 2010/11.