Saliyo ta dakatar da kyaftin dinta

Ibrahim Kargbo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallon ya karyata sa hannu a cinikin wasa

Hukumar kwallon kafar Saliyo ta dakatar da kyaftin dinta Ibrahim Kargbo, da kuma jami'ai 14 bisa zargin cinikin wasan kwallon kafa.

Daga cikin 'yan kwallo da aka dakatar bayan Ibrahim Kargbo, akwai Samuel Barley da Christian Caulker.

Sauran wadan da aka dakatar sun hada da alkalan wasa uku da jami'ai takwas cikinsu har da Rodney Micheal.

Ana zargin 'yan wasan ne da jami'ai bisa cinikin wasa da ya shafi Kasar Afirka ta kudu a wasan sha re fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2008, inda aka tashi wasa babu ci.