Demba Ba na gab da koma wa Besiktas

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba ya zura kwallaye 17 a kakar wasan da ta wuce

Dan kwallon Senegal wanda ke murza leda a Chelsea Demba Ba na gab da kulla yarjejeniya da Besiktas ta Turkiya a kan fan miliyan takwas.

Dan shekaru 29, ya isa birnin Istanbul don a gwada lafiyarsa kafin ya sanya hannu a kwanigilar.

Ya bayyana a shafinsa na Twitter "Sauran kadan a kamalla komai kafin in sanya hannu."

Tsohon dan kwallon Newcastle, Ba ya soma wasanni 23 daga cikin 51 da ya buga wa Chelsea sannan ya zura kwallaye 14.

Tuni Chelsea ta siyo Diego Costa daga Atletico Madrid a kan fan miliyan 32 sannan kuma a cikin 'yan wasan gaba akwai Fernando Torres.

Karin bayani