Ingila ta fado mataki na 20 a jerin Fifa

England Ranking
Image caption Ingland ta fado matsayi na 20 daga matakin na 10 a Fifa

Ingila ta fado matsayi na 20 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, wanda Fifa ta fitar da sakamakon watan Yuni.

Rashin kokarin kasar ne a gasar cin kofin duniya, yasa ta koma mattaki na 20, wacce take biye a bayan Bosnia-Hercegovina da Costa Rica da the Amurka.

Spain wacce take matsayi na daya a duniya ta koma ta takwas, inda Jamus zakarar kofin duniya ta dare matsayi na daya.

Scotland ta ci gaba da zama a matsayi na 27, yayin da Wales ta fado matsayi na 44. Ireland ta Arewa na mataki na 89 inda Jamhuriyar Ireland ta ci gaba da zama a matakinta na 70.

Ga jerin kasashe 10 da ke kan gaba a iya taka kwallo a duniya.

1 - Germany 2 - Argentina 3 - Netherlands 4 - Colombia 5 - Belgium 6 - Uruguay 7 - Brazil 8 - Spain 9 - Switzerland 10 - France