Newcastle United ta dauko Riviere

Emmanuel Riviere Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallo na biyar da Newcastle ta dauko a bana

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United, ta dauko dan kwallon Monaco Emmanuel Riviere, mai zura kwallo a raga a yarje-jeniyar kwantaragi mai tsawo.

Riviere, mai shekaru 24 dan kwallon Faransa ya koma kulob din ne kan kudi da zai kai fan miliyan 5.

Dan wasan ya zamo na biyar da kulob din West Ham ya dauka a bana, bayan Remy Cabella da Ayoze Perez da Jack Colback da Siem de Jong.

Riviere, ya zura kwallaye 40 a raga daga cikin wasanni 161 da ya bugawa Monaco wasanni.