Nigeria ta cika sharudan Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aminu Maigari da sauran jami'an Fifa son koma kan aiki

Nigeria ta cika sharudan Fifa don janye dakatarwar da aka yi wa kasar daga shiga harkar kwallon kafa, bayan da wata kotu ta soke hukuncin dakatar da jami'an hukumar NFF.

Fifa ta dakatar da Nigeria daga shiga harkar kwallon kafa sakamakon katsalanda daga wajen gwamnatin, abinda ya sa kantoma ya maye gurbin zabbabbun jami'an NFF.

An baiwa Nigeria wa'adi zuwa 17 ga watan Yuli don ta canza shawarar dakatar da jami'an NFF.

Bisa wannan matakin, a yanzu Nigeria za ta iya halartar gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasada shekaru 20 da kuma gasar cin kofin 'yan kasada na shekaru 17 na Afrika.

BBC ta fahimci cewar Sakatare Janar na NFF, Musa Amadu tuni ya aike wa Fifa bayani game da wannan matakin na maidoda su kan kujerunsu.