Enner Valencia ya koma West Ham

Enner Valencia
Image caption West Ham ta sha gwagwarmaya kafin daukar dan wasan

Kulob din West Ham ya dauko dan kwallon Ecuador, Enner Valencia akan kudi da ya kai fan miliyan 12 bisa kwantiragin shekaru biyar.

Valencia, mai shekaru 24 ya zura kwallaye uku a gasar cin kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci, inda ya zura kwallaye biyu a ragar Honduras kwallo daya a ragar Switzerland.

A wani jawabi da kulob din ya wallafa a sashin intanet yace "sun yi gogayya da wasu kungiyoyin Turai da suka yi zawarcin dan wasan kafin ya amince zuwa West Ham".

Dan wasan ya bugawa kulob din Emelec wasanni sama da 100, kafin ya koma Pachuca a watan Janairu.