Brazil zata nada sabon koci ranar Talata

Luiz Felipe Scolari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Brazil na shirin nada kocin da zai jagoranci kasar 2018

Brazil za ta nada sabon kocin tawagar 'yan kwallon kasar ranar Talata domin maye gurbin Luiz Felipe Scolari wanda ya ajiye aikinsa.

Scolari, mai shekaru 65, wanda ya jagoranci Brazil kaiwa wasan daf dana karshe a kofin duniya da kasar ta karbi bakunci, ya gamu da cikas a dokewar da Jamus ta yi musu da ci 7-1.

Tuni ake rade-radin cewa tsohon kocin kasar Dunga, wanda ya horas da tawagar yan wasa daga shekarun 2006 zuwa 2011,kila ya karbi aikin.

Sauran masu horaswa da ake hangen maye gurbin Scolari, sun hada da kocin Corinthians Tite da mai horas da Sao Paulo Muricy Ramalho da kuma Vanderlei Luxemburgo wanda ya jagoranci kasar daga 1998 zuwa 2000.