Davies na daf da komawa Tottenham

Ben Davies Hakkin mallakar hoto Huw Evans Picture Agency
Image caption Tottenham na shirin taga ta taka rawar gani a Premier

Dan kwallon Swansea mai tsaron baya Ben Davies, ya bar sansanin atisayen kungiyar a Amurka a yunkurinsa na komawa Tottenham.

Cikin kunshin yarje-jeniyar da suka kulla, dan kwallon Spurs Gylfi Sigurdsson, mai shekaru 24, zai koma kulob din Swansea.

Haka kuma Tottenham na sha'awar daukar mai tsaron ragar Swansea golan Netherlands Michel Vorm.

Vorm, mai shekaru 30, yana cikin tawagar 'yan kwallon Holland da suka kare a matsayi na uku a gasar cin kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci.