Drogba zai kara koma wa Chelsea

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mourinho ya ce har yanzu da sauran Drogba

Didier Drogba na duba yiwuwar koma wa Chelsea domin kulla yarjejeniyar shekara daya tare da kungiyar.

Dan wasan kasar Ivory Coast wanda yarjejeniyarsa ta kare a Galatasaray a kakar wasan da ta wuce, ya bar Stamford Bridge a shekara ta 2012.

Dan shekaru 36, bisa dukkan alamu za a baiwa Drogba damar zuwa Chelsea a matsayin dan wasa kuma koci.

Drogba ya lashe kofuna uku na gasar Premier da kuma kofuna hudu na FA da League daya da kuma gasar Zakarun Turai tare da Chelsea.

A shekara ta 2004 ya koma Chelsea daga Marseille a kan fan miliyan 24.