Gerrard ya yi ritayar wasa a Ingila

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Gerrard ya bugawa Ingila wasanni 114 ya zura kwallaye 21

Kyaftin din tawagar Ingila Steven Gerrard, ya yi ritayar bugawa kasarsa kwallo bayan da ya buga mata wasanni 114.

Gerrard, mai shekaru 34, ya fara bugawa Ingila wasa lokacin da kasar ta doke Ukraine daci 2-0 a shekarar 2000.

Dan kwallon mai wasan tsakiya ya zura kwallaye 21, daga cikin manyan gasar wasanni shida da ya buga.

Gerrard, ya bugawa Ingila wasansa na karshe a karawar da suka tashi wasa babu ci da Costa Rica a gasar kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Dan wasan zai maida hankali wajen bugawa kulob dinsa Liverpool wasanni, wanda ake hangen kila hukumar kwallon kafar kasar ta bashi ambasada na kwallon kafa.