Negredo ya karya kafarsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Negredo ya ce ba ya son ya bar Etihad

Dan kwallon Manchester City Alvaro Negredo zai yi jinyawar wasu watanni sakamakon karayar da ya samu a kafarsa.

Dan shekaru 28, ya karya kafa a lokacin wasan sada zumunci tsakaninsu da Hearts a ranar Juma'a.

Negredo ya ce "Zan yi jinyawar wasu watanni amma zan dawo da karfi na."

Dan wasan ya koma City ne daga Sevilla a shekara ta 2013 inda ya zura kwallaye 26 a kakar wasan da ta wuce.

Manchester City za ta tafi birnin Kansas domin soma rangadi a Amurka kafin soma kakar wasa mai zuwa.