'Yan wasa 6 sun ki komawa Donetsk

Shakhtar Donetsk Stadium Hakkin mallakar hoto shakhtar.com
Image caption 'Yan wasan na fargabar kada tashin hankali ya rutsa da su

Kimanin 'yan wasa shida ne suka ki komawa kulob dinsu Shakhtar Donetsk a Ukraine domin tunkarar karawar da kulob din zai yi a Faransa ranar Asabar.

'Yan wasan na fargabar yadda ake samun karuwar tashe-tashen hankula a birin da kulob din yake da zama.

Sai dai mai kungiyar Rinat Akhmetov, ya gargadi 'yan wasan da suka hada da 'yan kasar Brazil biyar da dan kwallon Argentina daya cewa za a ci tararsu Yuro miliyan da dama idan basu koma ba.

Akhmetov, ya kara tabbatarwa da 'yan wasan cewar za'a kare lafiyarsu.

Hukumar gudanar da gasar wasan kwallon kafar Ukraine na fatan fara gasar cin kofin bana ranar Juma'a duk da tashin hankalin da ake yi a kasar.