Stoke City ta dauko Bojan daga Barcelona

Bojan Krkic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bojan ya bugawa Spaniya wasa, yanzu ya koma Serbia

Kulob din Stoke City ya kammala dauko dan kwallon Barceloan Bojan Krkic kan kwantiragin shekaru hudu.

Krkic, mai shekaru 23, ya fara bugawa Barcelona kwallo yana da shekaru 16, amma bai sake bugawa kulob din wasa ba, bayan da ya koma roma shekaru biyu baya.

Ya kwashe kakar bara a Ajax aro, inda ya buga wasanni 24 ya kuma zura kwallaye shida.

Kikic ya bugawa Spaniya wasa daya kacal a shekarar 2008, bayan da Serbia ta gayyato shi buga wa tawagar kasar wasanni.