Dunga ya sake zama kocin Brazil

Dunga Brazil Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sake nada Dunga a sabom kocin Brazil karo na biyu

Kasar Brazil ta bayyana tsohon dan kwallonta Dunga, a matsayin sabon kocin tawagar kasar a karo na biyu.

Dunga wanda ya zama kyaftin din Brazil a gasar cin kofin Duniya a shekarar 1994 inda suka yi nasarar lashe gasar, wanda ya taba horas da kasar daga shekarar 2006-2011.

Sabon kocin mai shekaru 50, wanda ke sha'awar kama aikin ya ce, "Na yi matukar farin ciki da sake dawo wa a matsayin kocin kasar."

Dunga ya maye gurbin Luiz Felipe Scolari ne, wanda ya yi murabus bayan da Brazil ta kai wasan daf da na kusa da karshe amma ta sha kashi a hannun Jamus da ci 7-1.