UEFA: Ta hukunta Paris St-Germain

Paris St-Germain Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karon farko da UEFA ta hukunta PSG kan batun cin zarafin nakasassu

Hukumar gudanar da gasar wasan kwallon Turai (UEFA) ta umurci PSG, ta rufe sashin 'yan kallon wasanta mai suna Parc des Princes, a lokacin da za ta kara a gasar kofin Zakarun Turai.

Hukuncin da hukumar ta dauka ya biyo bayan korafin da wasu guragu magoya bayan Chelsea suka shigar da cewa an ci zarafinsu a kakar bara.

Guragun magoya bayan kulob din Chelsea, sun ce an ci zarafinsu ne ranar 2 ga watan Afrilu a karawar wasan daf da na kusa da karshe.

Daya daga guragun mai goyon bayan Chelsea, mai amfani da keken guragu Lisa Hayden, tace 'Ban ji dadin yadda aka karbe mu ba, har ma nayi tunanin kada a taba lafiyarmu' .

Wannan ne karon farko da aka hukunta kulob din, kan batun cin zarafin nakasassu.