Caroll ya ji rauni a wurin atisaye

Andy Carroll
Image caption Dan kwallon ya sha jinya a kakar wasan bara

Dan kwallon West Ham Andy Caroll, ya ji rauni a sawunsa lokacin da suke atisaye a New Zealand.

Dan kwallon bai buga wasan da Wellington Phoenix ta doke su da ci 2-1 ba, sannan ba zai buga karawar da za suyi da Sydney a Wellington ranar Asabar ba.

Kulob din ya fitar da wata sanarwa ta Intaner cewa 'Carroll zai yi jinya ta musamman domin ya samu saukin tunkarar buga kakar wasan Premier bana.

Dan wasan mai shekaru 25, ya yi fama da jinya a kakar bara, dalilan da yasa Ingila bata gayyace shi tawagar 'yan wasanta ba.

Sabon dan kwallon da kulob din ya dauko Zarate, shi ne ya zura kwallo a karawar da aka doke su da ci 2-1.