Nigeria za ta sake dauko Stephen Keshi

Stephen Keshi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption NFF na son tattaunawa da Keshi domin ya sake horas da Super Eagle

Hukumar kwallon kafa ta Nigeriya (NFF) ta bayyana cewa za ta tattauna da Stephen Keshi, domin ta rarrashe shi ya sake karbar kocin Super Eagles.

Tun farko hukumar ta bari kwantiraginsa ya kare bayan kammala gasar cin kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci ba tare da tsawaita masa aikinsa ba.

Koda yake Ministan wasanni na Nigeria ya hangi abinda Keshi ya bukata da gwamnati ta biya shi da cewar ya yi matukar yawa.

Kocin mai shekaru 52, ya jagoranci Nigeria lashe kofin Nahiyar Afirka karo na uku, bayan da kuma ya kai tawagar kasar zagaye na biyu a gasar cin kofin Duniya.

Keshi ya yi ritaya dangane da matsalolin kudi da ya sha fama da rashin biyansa albashi a kai-akai da batun tsoma masa baki wajen gayyato 'yan wasan tawagar kasar.