Fred ya koma kulob dinsa Donetsk

Fred Brazil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya hakura ya koma kulob dinsa Donetsk

Dan kwallon Brazil Fred, ya koma kulob dinsa Shakhtar Donetsk, bayan da kungiyar ta koma da wasanninta birnin Kiev.

Fred, mai shekaru 21, yana daga cikin 'yan wasa 6 da basu koma Donetsk ba, bisa fargabar tashin hankalin dake faruwa a Ukraine.

Kulob din Donetsk na jiran komawar mai tsaron baya Ismaily nan da 'yan kwanaki masu zuwa, amma Douglas Costa da Alex Teixeira da Dentinho da Facundo ba a san ranar da za su koma ba.

Babban jami'in kulob din Sergei Palkin ya ce 'Yawancin 'yan wasan suna fargabar rikicin dake faruwa a kasar ne, mu kuma muna ta kokarin nuna musu cewa babu abinda zai taba lafiyarsu.

'Yan wasan shida sun ki barin Faransa a makon jiya, bayan da kulob din ya buga wasan sada zumunci, domin kaucewa rikici tsakanin 'yan tawaye masu goyon bayan Rasha da dakarun gwamnatin Ukraine.