Man City ta sayi Eliaquim

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Eliaquim Mangala bai buga wa Faransa kwallo ba a gasar cin kofin duniya

Manchester City ta fitar da wani faifan bidiyo wanda ga alamu yake nuna dan wasan baya na kulob din FC Porto, Eliaquim Mangala na sanya hannu don koma wa kungiyar.

Ana alakanta dan wasan na kasar Faransa mai shekaru 23, da yarjejeniyar fam miliyan 32 zuwa City, kuma an gan shi a Manchester wannan makon amma babu wata sanarwa da aka fitar.

Sai dai wani hoton bidiyo a shafin intanet na kulob din wanda amma tuni aka cire ya nuna yadda ake yi wa dan wasan gwajin lafiya.

Kungiyar Man City ta ce an yi satar shiga shafin intanet dinta, kuma bai kamata a ce bidiyon ya fita ba tun kafin a kammala yarjejeniyar.

Wani hoton bidiyon tashar talbijin din Man City ya nuna saukar wani jirgi a filin jiragen sama na Manchester dauke da taken "Karfe 9 na safe, dan wasan baya na kasar Faransa Eliaquim Mangala ya sauka a Manchester."