Drogba dan Chelsea ne - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Drogba ya haskaka a zamansa a Chelsea

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce Didier Drogba dan kulob din ne kuma suna tunanin kara sayen dan kwallon.

Dan wasan Ivory Coast mai shekaru 36, ya lashe kofuna goma tare da Chelsea daga 2004-2012 kuma kwangilarsa ta kare da Galatasaray.

Mourinho ya ce kulob din na tunanin kulla yarjejeniya da shi, kuma za a yanke hukunci ne ta bin hanyar 'yar gida.

Yace "Zan sake dawo da shi dan wasa ne mai kwazo da gogewa".

Drogba ya hade da Chelsea daga Marseille a kan fan miliyan 24 a shekara ta 2004, inda ya lashe kofunan gasar Premier uku da na FA hudu da na League biyu da kuma na zakarun Turai guda daya.

Ya bar kulob din a shekara ta 2012 bayan da ya ci fenariti a wasan da Chelsea ta doke Bayern Munich a gasar zakarun Turai.

Karin bayani