Liverpool ta dauko Divock Origi

Divock Origi Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sai a kakar wasan badi ne dan kwallon zai koma Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kammala daukar Divock Origi, dan wasan Belgium daga kulob din Lille ta Faransa kan kudi fan miliyan 10.

Dan wasan mai shekaru 19 da haihuwa, ya rattaba kwantiragin shekaru biyar, amma zai ci gaba da wasa a Faransa aro, sai kakar badi ne zai koma Anfield buga kwallo.

Origi, ya bugawa Belgium wasanni biyar da ta kara a gasar cin kofin Duniya da Brazil ta dauki bakunci, shi ne ya zura kwallo a wasan da suka doke Rasha da ci daya mai ban Haushi.

Dan wasan ya zamo dan kwallo na shida da kulob din Liverpool ya dauko bayan Rickie Lambert da Adam Lallana da Dejan Lovren daga Southampton, da kuma Emre Can daga Bayer Leverkusen da Lazar Markovic daga Benfica.