Premier: Za a fara amfani da fentin rafli

Refree Spray Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alkalan wasan Premier suma za su fara amfani da fenti mai saurin bushewa

Za a fara amfanin da fenti mai saurin bushewa, irin wanda alkalan wasa suka yi amfani da shi a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Alkalan wasa na amfani da fentin ne wajen shata inda za'a buga kwallo idan an yi laifi da wurin da 'yan wasa za su bada tazarar buga kwallon.

Mahukuntan gasar Premier sun ce tun farko ba su yi tunanin fara amfani da fentin a wasannin Premier ba, sai da suka fuskanci alfanun yin hakan.

Alkalan Brazil dana Argentina sun dade suna amfani da fentin mai saurin bushewa a gasar wasanninsu, wanda za kuma a fara yin amfani da shi a gasar cin kofin Zakarun Turai a badi.

Fenti da yake saurin bushewa da zarar alkalin wasa ya fesa shi, yana taimaka musu wajen hana 'yan wasa gusawa daga wajen da alkali ya umarci 'yan wasa su tsaya.