Renard ya zama kocin Ivory Coast

Herve Renard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya taba lashe kofin Nahiyar Afirka da Zambia

Kasar Ivory Coast ta dauko Herve Renard, a matsayin sabon kocin da zai horas da tawagar 'yan kwallon kasar.

Renard ya maye gurbin Sabri Lamouchi, wanda ya ajiye aiki bayan gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Kocin mai shekaru 45 da haihuwa ya jagoranci kasar lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2012.

Nasarorin da ya samu a Afirka yasa ya doke abokan zawarcin horas da tawagar Elephants da suka hada da Frederic Antonetti da Manuel Jose.

Kalubalen da ke gaban kocin shi ne ya kai Ivory Coast gasar cin kofin Nahiyar Afirka da Morocco za ta karbi bakunci a badi.

Renard ya yi ritaya daga horas da Zambia a shekarar 2013, ya koma Sochaux ta Faransa inda kulob din ya fadi zuwa gasar Ligue 2 a watan Mayu.