Adidas ya gargadi Manchester United

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabon kocin na kokarin dawo da tagomashin kulob din

Kamfanin Adidas ya gargadi Manchester United cewa zai zabtare kaso 30 cikin dari idan har kulob din bai koma buga gasar cin kofin zakarun Turai ba daga shekarar 2015-16.

Kamfanin Jamus da ya rattaba kwantiragi da United mafi tsoka a duniya kan kudi fan miliyan 750, ya kuma ce zai soke yarje-jeniyar da suka kulla idan kulob din ya bar buga gasar Premier.

United ta kasa samun tikitin buga kowacce irin gasar kofin zakarun Turai a bana, bayan da ta kare a matsayi na bakwai a teburin Premier.

Tuni kulob din ya dauko sabon koci Louis van Gaal mai shekaru 62, wanda ya maye gurbin David Moyes