Man United za ta sayar da hannun jari

Malcom Glazer Family Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Karo na biyu kenan da za su sayar da hannun jarin kulob din

Mamallakan kulob din Manchester United, iyalan Glazer za su sayar da hannun jarin kungiyar a kasuwar shunku ta Amurka da za su samu sama da fan miliyan 88.

Kungiyar ta sanar da cewa za a sayar da hannun jarin miliyon takwas da zai kai kaso biyar cikin dari daga cikin kasuwancin kulob din.

Iyalan Glazer za su ci gaba da jagorantar United, wanda tun a baya sun taba sayar da kaso 10 cikin 100 a shekarar 2012.

A yanzu 'ya'yan marigayi Malcolm Glazer ne su shida ke da United, ana kuma hada-hadar hannun jarin kungiyar kan sama da dala 19.

Glazer ya sayi United ne kan kudi fam miliyan 790 a shekarar 2005.