Keshi zai kara koma wa Super Eagles

Image caption Stephen Keshi

Hukumar kwallon Nigeria-NFF ta bayyana cewar tana gab da kulla sabuwar yarjejeniya da Stephen Keshi domin ya sake jan ragamar tawagar Super Eagles.

Dan shekaru 52, Keshi ya jagoranci Nigeria ta lashe gasar cin kofin Afrika a karo na uku a shekara ta 2013 sannan kuma ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya a Brazil.

An kira taron gaggawa na jami'an hukumar NFF domin tattauna batun baiwa kocin sabuwar kwangila.

BBC ta fahimci cewar za a dunga baiwa Keshi albashin kusan $43,250 a duk wata, fiye da albashinsa na baya watau $30,900.

Ana tunanin Keshi zai kulla yarjejeniyar shekaru da Nigeria idan har aka sasanta batun kwangilar.

Karin bayani