Seychelles ta soke wasanta da Saliyo

Seychelles Health
Image caption Seychelles ta hakura da karawa da Saliyo

Seychelles ta soke karawar da za tayi da Saliyo a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, bisa tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Hakan na nufin ta barwa Saliyo wasan da kuma gurbinta na neman cancantar shiga gasar kofin Afirka da Morocco za ta karbi bakunci a badi.

Tun ranar Alhamis aka sanar da sashin wasanni na BBC cewa mahuntan Saliyo sun hana tawagar 'yan wasa shiga jirgi a Kenya da ya kamata ya kai su Seychelles domin fafatawa a wasa na biyu.

Hukumar shige da fice ta Seychelles ce ta hana tawagar kasar ziyartar wasan, don kauce wa yada cutar.

Tuni shugaban Saliyo ya kaddamar da dokar ta-baci da nufin shawo kan matsalar yaduwar cutar Ebola.