Danny Rose ya tsawaita kwantiraginsa

Danny Rose Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Danny Rose

Dan kwallon Tottenham Danny Rose, ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar na tsawon shekaru biyar.

Rose, mai shekaru 24 da haihuwa ya buga wasanni 38 tun lokacin da ya koma Spurs daga kulob din Leeds a shekarar 2007.

Dan wasan mai tsaron baya ta hagu, zai yi gogayya da sabon dan kwallon da kungiyar ta sayo Ben Davies daga Swansea.

Rose ya buga wasa aro a kungiyar Watford da Peterborough da Bristol City da Sunderland,