Tottenham za ta siyo Eric Dier

Dier haifaffen Ingila ne

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Dier haifaffen Ingila ne

Kungiyar Tottenham ta amince ta kulla yarjejeniya da dan wasan Sporting Lisbon Eric Dier kan kudi fam miliyan 4, amma sai an gwada lafiyarsa.

Dan wasan tawagar 'yan kasa da shekara 21 a Ingila , haifaffan Cheltenham, amma ya koma Portugal tun yana karami, ya bugawa Lisbon wasanni 30.

Dier, mai shekaru 20, ya nuna jan kafa wajen kulla sabuwar yarjejeniya da Lisbon, bayan da Tottenham ta bada tayin sa a kan Euro miliyan 5.

Shi ne na uku a jerin 'yan wasan da Tottenham ta dauka a wannan bazarar bayan Ben Davies da Michel Vorm na kulob din Swansea.