Jenkinson ya koma West Ham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Carl Jenkinson zai shafe kakar wasan 2014/2015 a West Ham

Kulob din West Ham ya kabi aron dan wasan bayan Arsenal Carl Jenkinson na tsawon shekara guda.

Dan wasan mai shekaru 22, ya yi wasanni a kungiyoyi da dama a gasar Premier, amma a karshe ya tsaya a West Ham.

Jenkinson ya ce, "Ina kallon cewa wannan muhimmin al'amari ne zuwa na kulob din, ina kuma fatan zan kara samun kwarewa domin wannan shekara na da muhimmanci a gare ni."

Dan wasan ya samu koma baya ne a Arsenal biyo bayan manyan 'yan wasan baya irin su Mathieu Debuchy mai shekaru 29 da Calum Chambers mai shekaru 19 sun kulla kwantaragi da kulob din na Arsenal.

Jenkinson, wanda ya ci wa Ingila kwallo daya, ya kuma buga wa Arsenal wasanni 22 a Gasar kakar bara.

Karin bayani