Inter Milan za ta dauko Gary Medel

Gary Medel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cardiff na shirin ganin ta sake komawa gasar Premier

Kulob din Cardiff City ya amince da tayin fan miliyan 10 da kungiyar Inter Milan ta yiwa dan wasanta Gary Medel.

Abinda ya rage yadda Inter Milan za ta tsara biyan Cardiff City kudin dan kwallon.

Haka kuma Bluebirds ta ki amincewa da tayin fan miliyan biyar da Queens Park Rangers ta yiwa dan wasanta Jordon Mutch.

Cardiff na shirin kara dauko 'yan kwallo hudu kafin ta kara a wasan 'yan rukuni na daya da za ta fafata da Blackburn Rovers ranar 8 ga watan Agusta.

Medel dan kwallon Welsh shi ne dan wasa mafi daraja da Bluebirds ta sayo daga Sevilla kan kudi fan miliyan 11 a Agustan bara.