Man United ta doke Madrid 3-1

United vs Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta lashe wasanni hudu a Amurka data buga

Kulob din Manchester United ya doke Real Madrid mai rike da kofin zakarun Turai 3-1 a gaban 'yan kallo 109,318 a Amurka.

Ashley Young ne ya zura kwallaye biyu a ragar Madrid daga baya Javier Hernandez ya kara kwallo ta uku, hakan ya bai wa United nasarar lashe wasanni hudu da ta buga a Amurka.

Dan wasa Gareth Bale ne ya farkewa Madrid kwallo daya a dukan daga kai sai mai tsaron raga.

United za ta kara da Liverpool ranar Litinin a wasan karshe na cin kofin International Champions Cup, bayan da Liverpool ta doke AC Milan da ci 2-0.

Sabon kocin United Louis van Gaal, ya jagoranci kulob din lashe wasanni hudu da kungiyar ta buga a Amurka.