Newcastle ta dauko Ferreyra aro

Facundo Ferreyra Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle za ta iya sayen dan kwallon idan ya taka leda mai kyau

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ta dauko dan wasan Shakhtar Donetsk Facundo Ferreyra aro har zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan Argentina, mai shekaru 23 da haihuwa, na daya daga cikin 'yan kwallon Shakhtar shida da suka ki komawa Donetsk bisa dalilan tashin hankali a Ukraine a watan jiya.

Kocin Newcastle Alan Pardew ya ce "Facundo kwararren dan wasa ne da ya yi fice ake kuma girmamawa a Argentina".

Ferreyra ya zama dan kwallo na bakwai da Pardew ya dauko, sannan za su iya sayen dan kwallon idan ya taka leda mai kyau a kulob din.

Dan wasan ya zura kwallaye shida a wasanni 22 da ya buga wa Shakhtar a bara, bayan da kungiyar ta sayo shi fan miliyan shida daga Velez Sarsfield a watan Yulin July 2013.