Visa ta kawo wa Brown Ideye cikas

Brown Ideye Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan yana sa ran komawa kulob din nan bada dadewa ba.

Sabon dan kwallon West Bromwich Albion Brown Ideye, ya ce takardar samun izinin shiga Birtaniya ce tayi masa cikas din komawa kulob din.

Dan kwallon Najeriya, mai shekaru 25 da haihuwa, an sayo shi daga Dynamo Kiev tun 18 ga watan Yuli, amma har yanzu bai samu izinin shiga Birtaniya ba.

Ideye bai samu halartar karawar da West Brom tayi da Nottingham Forest a makon jiya, kuma ba zai buga fafatawar da kulob din zai yi da Port Vale ranar Talata ba.

Dan wasan ya buga wasanni 182 inda ya zura kwallaye 74, kafin ya koma West Bromwich Albion da ya kai kudi fan miliyan 10.

Ideye, wanda ya buga kofin zakarun Turai Champions League da Europa League, ya zura kwallaye biyar a wasanni 24 da ya bugawa Najeriya.