Man City za ta biya Lampard Albashi

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwqallon zai bar Man City a watan Janairu

Kulob din Manchester City zai biya Frank Lampard albashi na tsawon watannin da zai bugawa kungiyar wasa aro.

Lampard, mai shekaru 36 da haihuwa ya rattaba kwantiragi da New York City a watan jiya, wanda sai a watan Maris ne za'a fara gasar cin kofin Amurka.

Tuni kocin Arsenal Arsene Wenger ya zargi yadda ake cuku-cukun kwantiragin dan kwallon, inda ya ce kulob din na kokarin karya ka'idojin cinikin 'yan wasan Turai, kamar yadda aka sami kulob din da laifi a baya.

Wenger ya ce "City tana amfani da wasu kungiyoyi mamallakan ta domin saya mata 'yan wasa, har ma yace ana rade-radin za'a saya wa City 'yan kwallo biyar".