Saliyo ta soke kwallo saboda Ebola

Sierra Leone Ebola Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Cutar Ebola mai saurin halaka al'umma

Hukumar kwallon kafar Saliyo ta dakatar da wasannin kwallon kafa a kasar a kokarin da take na kauracewa yada cutar Ebola.

Tuni shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya kaddamar da dokar ta baci da nufin shawo kan matsalar yaduwar cutar.

Ana sa ran za ayi wata guda zuwa kwanaki 90 wajen yaki da yaduwar cutar a kasar.

Hakan na nufin kasar ba za ta fafata a wasan neman gurbin shiga kofin nahiyar Afirka ba da Kamaru a watan gobe.

Haka kuma Saliyo ba za ta samu halartar wasan farko na rukuni na hudu da za ta kara da Ivory Coast ba.

Itama gasar cin kofin Premier Saliyo wasannin zagaye na biyu ba za'a ci gaba da wasannin ba.