Premier: Za a kafa dokar jin rauni a ka

Premier Head Injuries Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gasar Premier na son fara amfani da dokar a bana

Za a kafa sabuwar dokar da za ta rage matsalar jin rauni a ka, a gasar wasan kwallon kafa na cin kofin Premier a farkon kakar wasan 2014-15.

Idan dan wasa ya ji rauni a kansa dole ne ya bar filin wasa, kuma likitan kulob ne zai tantance idan dan kwallon zai iya komarsawa wasa ba mahukunta ba.

Kungiyar da ke karbar bakuncin wasa dole ne ya tanadi likitan ko ta kwana kafin a fara wasa.

A kakar bara, an ga sakacin kulob din Tottenham, da ya bar Hugo Lloris ya koma wasa bayan da ya gamu da buguwa a kansa a karawar da suka tashi babu ci da Everton.