Webb ya yi ritaya daga alkalancin wasa

Howard Webb
Image caption Web ya kwashe shekaru 25 yana alkalancin wasa

Howard Webb ya yi ritaya daga alkalancin wasan Kwallon kafa bayan da ya kwashe shekaru 25 yana aikin, an kuma nada shi daractan tsare-tsare na Kungiyar Alkalan Wasan Kwallon Kafa.

Webb ya alkalanci wasannin Premier sau 500, kuma yana daga cikin wadanda suka alkalanci Gasar kofin duniya da aka yi a Brazil.

Mai shekaru 43, ya fara Rafli a shekarar 1989 daga arewacin kasar Ingila daga nan ya koma alkalancin gasar League, sannan aka zabo shi zuwa kungiyar zababbun alkalai masu alkalancin wasannin Premier a shekarar 2003.

Webb ya halarci manyan gasar wasannin kwallon kafa sau tara, ya kuma alkalanci wasan karshe na cin kofin zakarun Turai, da kuma wasan karshe na kofuna da dama a Ingila.

A gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil ya alkalanci karawar da aka yi tsakanin Colombia da Ivory Coast da kuma afatawa tsakanin Brazil da Chile.